Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Har yanzu Najeriya tana da ragowar dama a gasar FIBA ta duniya
2019-09-02 10:50:19        cri

Keftin Ike Diogu, ya ce har yanzu kungiyarsa tana da ragowar dama ta kaiwa zagaye na gaba na kungiyoyi 16, duk da kasancewar Najeriyar ta sha kashi a hannun Rasha da maki 82-77 a gasar cin kwafin duniya ta wasan kwallon Kwando FIBA.

A yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Diogu yace, "a kowane wasa muna son cimma nasarar lashewa ne, babu wani karin matsin lamba da muka fuskanta. Kawai dai yanayi ne na wasan. Tilas ne mu lashe wasanni biyu; mun shirya tsallakawa mataki na gaba", matashin mai shekaru 35 da haihuwa ya bayyana hakan bayan kammala shirin samun horo da kungiyarsa a cibiyar wasanni ta Wuhan da yammacin ranar Lahadi.

Rasha ta sha da kyar a hannun Najeriya, inda ta samu maki 8 a zagaye na hudu wanda muhimmin mataki ne na neman lashe gasar cin kofin duniya. Tsohon dan wasan na NBA yayi nadama tare da takaici game da rashin galaba a wasan.

Kwararren dan wasan yace, "Mun koyi darasi daga kurakuren da suka faru amma a nan gaba idan mun kai matsayi irin wannan mun san hakikanin abinda zamu yi sabanin wanda muka yi a baya domin cimma nasarar lashe wasan".

Diogu yace yana hasashen Najeriya zata fafata da Sin a wasannin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China