Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyoyin 'yan bindiga a Najeriya sun hallaka mutane 1,460 cikin watanni 7
2019-08-30 10:17:32        cri

A ranar Alhamis gwamnatin Najeriya ta sanar cewa, hare-haren da mayakan 'yan bindiga suka kaddamar ya yi sanadiyyar kashe mutane 1,460 a shiyyar arewa maso yammacin kasar tsakanin watan Janairu zuwa Yulin bana.

Cikin wannan wa'adi, kungiyoyin 'yan bindigar sun kaddamar da hare-hare kimanin 330 a shiyyar, kamar yadda aka sanar a wani taron jami'an tsaro da aka kaddamar a jahar Kebbi dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Halin tsaron da shiyyar ke ciki a halin yanzu, wadda a lokacin baya take daya daga cikin shiyyoyi mafi zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, amma a yanzu al'amarin ya kasance babban abin damuwa ga hukumomin tsaron Najeriya da ma al'ummar kasar baki daya, a cewar Amina Shamaki, babbar sakatariya a ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Tun a farkon wannan mako, kafafen yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa gwamnoni 6 na shiyyar kudu maso yammacin Najeriyar suna shirin kafa wata rundunar tsaron musamman wacce aka ba ta suna hadaddiyar rundunar wanzar da tsaro ta yammacin Najeriya da nufin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi shiyyar.

Wannan mataki ya biyo bayan samun amincewar da ofishin babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar ya yi ne cewa a kafa rundunar wanzar da tsaro ta hadin gwiwa, da nufin kawo karshen yawan kashe-kashe, da hare-haren 'yan bindigar, da yin garkuwa da mutane a shiyyar kudu maso yammacin kasar.

Za a kaddamar da rundunar tsaron ta musamman a watan Oktoba, wacce za ta yi aikin hadin gwiwa da hukumomin tsaron kasar da nufin kawo karshen kalubalolin tsaron dake addabar shiyyar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China