Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 6 sun mutu 17 sun samu raunuka yayin da wata babbar mota ta kauce hanya a Najeriya
2019-09-03 12:41:17        cri
An tabbatar da mutuwar mutane 6 kana wasu 17 sun samu raunuka a sanadiyyar hadarin mota wanda ya rutsa da wata babbar mota da wasu kananan motoci 3 a jihar Anambra dake kudancin Najeriya, jami'in hukumar kiyaye haddura na yankin ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin.

Direban babbar motar wanda yayi lodin karafa makare a cikin motar, ya kasa sarrafa motar, inda ya bi ta kan wasu motoci uku akan hanyar Amawbia-Agulu zuwa Awka, babban birnin jahar, Andrew Kumapayi, kwamandan hukumar kiyaye haddura na shiyyar ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Gwamnan jahar Willie Obiano, wanda ya jagoranci tawagar jami'an bada agaji don kai dauki ga wadanda lamarin ya rutsa dasu, yace hadarin ya faru ne a kan titi mai matukar inganci wanda babu ramuka ko kadan a titin.

Ya bayyanawa 'yan jaridu cewa, abin takaici ne bisa yadda mutane suka rasa rayukansu a wannan hadarin, amma ya bada tabbacin za'a bada cikakkiyar kulawa ga wadanda suka samu raunuka.

'Yan sandan yankin sunce ana cigaba da binciken gano musabbabin hadarin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China