Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Xinjiang ta karbi sama da masu yawon bude ido miliyan 75 a rabin farko na bana
2019-07-31 10:13:57        cri

Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta karbi kimanin baki miliyan 75.9 a rabin farko na bana, adadin da ya karu kan na bara da kaso 46.

Shohrat Zakir, shugaban gwamnatin yankin ya bayyanawa wani taron manema labarai jiya a nan birnin Beijing cewa, jihar Xinjiang ta samu bunkasar bangaren yawon bude ido a shekarun baya-bayan nan. Ya ce adadin masu yawon bude ido da suka je Xinjiang ya zarce miliyan 150 a bara, wanda ya karu da kaso 40.1.

A cewar mataimakin shugaban Xinjinag, Erkin Tuniyaz, ana sa ran yankin zai yi maraba da sama da masu yawon bude ido miliyan 200 a bana.

Erkin Tuniyaz ya ce yankin ya lashi takobin mayar da Xinjiang matsayin muhimmin wurin yawon bude ido da zai yi fice a duniya. Ya ce mataki na gaba shi ne, kara inganta tsare-tsaren raya bangaren yawon bude ido da kokarin bullo da ingantaccen yanayin yawon bude ido da hidimomi da sufuri, tare da gaggauta gina ababen more rayuwa da za su taimakawa bangaren. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China