Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Hongkong ta yi Allah wadai da masu bore bisa amfani da karfin tuwo
2019-09-01 16:18:35        cri

Masu bore dake da tsattsauran ra'ayi sun yi gangami ba bisa doka ba a jiya Asaba tare da yin amfani da karfin tuwo. Mai magana da yawun gwamnatin yankin na musamman na Hongkong ya bayyana a daren wannan rana cewa, wasu masu bore sun kara tsanantar ayyukan nuna karfin tuwo, matakin da ya keta hakkin jama'ar wurin, hakan ya sa gwamnatin ta yi Allah wadai da su da kakkausar murya, kuma za a hukunta su yadda ya kamata.

Jami'in ya kara da cewa, masu boren sun yi biris da takardar da 'yan sanda suka bayar, sun taru ba bisa doka ba, da yin zanga-zanga a tsibiran Hongkong da Kowloon, har sun toshe hanyoyi, matakin da ya katse zirga-zigar tsibirin Hongkong, lamarin da ya kawo babbar illa ga zaman rayuwar jama'ar wurin. Ban da wannan kuma, masu zanga-zangar sun farma 'yan sanda da takalar gwamnatin yankin, sun jefa bam da suka hada da man fetur kan ginin hedkwatar gwamnati, da hedkwatar 'yan sanda, sannan sun kaiwa 'yan sanda hari da ruwan sinadarai da makamai masu karfi. Ban da wannan kuma, maso boren sun kunna wuta da lalata kayayyakin jama'a da kange hanyoyi da lahanta na'urorin manyan ayyukan more rayuwa da sauransu.

Jami'in ya ce, masu boren sun tada zaune tsaye a yankin, matakin da ya kawo barazana kwarai ga lafiyar 'yan sanda da jama'a. Gwamnatin za ta yi kokarin kiyaye zaman doka da oda, kuma ta yi kira ga jama'a da su bayyana rashin jin dadinsu kan wadanan ayyukan nuna karfin tuwo ciki hadin kai don dawo da kwanciyar hankali a yankin tun da wuri. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China