Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jackie Chan: Ina fatan za a hanzarta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankalin Hong Kong
2019-08-14 13:36:59        cri

 

Shahararren tauraren fina-finai na kasar Sin Jackie Chan ya shedawa manema labarai kwanan baya cewa, bai ji dadin abubuwan dake faruwa a baya-bayan nan a Hong Kong ba, saboda haka ya shiga aikin nan da ake kira "Mutane biliyan 1.4 masu rajin kiyaye tutar kasar Sin", da zummar bayyana kaunarsa a matsayinsa dan Basine kuma yankin Hong Kong, yana fatan kuma yada tunanin jama'a na tsaron dinkuwar kasa da kwanciyar hankali a kasar.

Ya ce, tsaro da zaman lafiya kamar iskar shaka ne ga jama'a, sai babu ita kafin a fahimci muhimmancinta. Ya ce Hong Kong, garinsa ne, kuma kasar Sin kasarsa, yana kaunar kasar Sin kuma yana kaunar garinsa, yana fatan za a gaggauta dawo da kwanciyar hankali a yankin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China