Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Magoyan bayan shirin "Mutane biliyan 1.4 masu rajin kiyaye tutar kasar Sin" sun zarce biliyan 5 a kan Intanet
2019-08-16 11:11:49        cri

An tada zaune tsaye a yankin musamman na Hong Kong a kwanakin baya, har wasu masu bore sun jefa tutar kasar Sin cikin teku, lamarin da ya janyo fushin Sinawa masu kishin kasa da kaunar yankin kwarai da gaske. Saboda haka, gidan talabijin na CCTV ya gabatar da shiri mai taken "Mutane biliyan 1.4 masu rajin kiyaye tutar kasar Sin" a kan Intanet, tare da samun mabiya fiye da biliyan 5.

Wani dalibin jami'a dake goyon bayan shirin Wang Yao ya ce, tilas ne a nuna kin amincewa da ko wani mataki na cin fuskar tutar kasar Sin da keta ikon mulkin kasar. Ita kuwa lauya Sun Haiyang, cewa ta yi, ba za ta yarda da cin fuskar tutar kasar ba, kuma ta yi imanin cewa, za a gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.

Wasu mutane masu martaba sosai a cikin al'umma, su ma sun mara baya ga shirin, don bayyana matsayinsu. Shahararren tauraron fina-finai na kasar Sin Jackie Chan ya ce, bai ji dadin abubuwan dake faruwa a baya-bayan nan a Hong Kong ba, ya yada wannan shiri nan take a kan shafinsa na Weibo don bayyana kaunarsa a matsayinsa na Basine kuma dan yankin Hong Kong, ya ce, tsaro da zaman lafiya kamar iskar shaka ne ga jama'a, sai babu ita sannan za a fahimci muhimmancinta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China