Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hongkong ta yi Allah wadai da kara tsanantar ayyukan masu zanga-zanga
2019-08-26 14:07:42        cri

Mai magana da yawun yankin musamman na Hongkong na kasar Sin ya mayar da martani a sassafe yau Litinin kan zanga-zangar da aka yi a Kwai Tsing da Tsuen Wan da dai sauran wurare na yankin a jiya Lahadi, inda ya ce, keta dokoki da nuna karfi da wadannan masu bore suka yi ya kara tsananta, kuma ya jefa Hongkong cikin wani mawuyacin hali mai hadari. Lamarin da ya sa gwamnatin yankin ta yi tir da shi da kakkausar murya, kana 'yan sanda za su gudanar da aikinsu yadda ya kamata don magance lamarin. Gwamnatin kuma ta yi kira ga jama'a da su hada kansu don dakile ayyukan keta dokoki da kiyaye doka da oda ta yadda za a dawo da zaman lafiya tun da wuri. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China