Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a hukunta masu tada zaune tsaye a Hongkong
2019-08-30 13:29:11        cri

An cafke masu tada zaune tsaye a Hongkong, wato Chen Haotian a daren jiya, lokacin da yake yunkuri gudu zuwa Japan, da Huang Zhifeng da kuma mambar kungiyarsa Zhou Ting a safiyar yau, bisa laifufukan da suka aikata.

Wadannan madugu biyu sun kasance a inuwa guda tare da wasu masu bore a Hongkong, wadanda ke neman kawo baraka a yankin, mumunan matakan da suka dauka sun hada da zuga jama'a su nuna kiyayya ga 'yan sanda, da tsai da shirin nuna karfin tuwo da rura wuta kan matasa da su yi zanga-zanga, har ma da yunkurin hambarar da mulkin gwamnatin yankin na musamman, baya ga haka da kuma shafa kashin kaji da kai hari kan gwamnatin tsakiya yadda suke so. Ban da wannan kuma, sun hada baki da karfin Turawa ciki hadda Amurka, har suka nemi 'yan siyasar ketare da su sa hannu kan harkokin yankin. A hakika dai sun lahanta yanayin yankin bisa fakewa da sunan kaunar yankin, sun kasance maciya amanar yankin, inda suke yunkurin mayar da Hongkong matsayin fagen daga tsakanin kasa da kasa, har zama wani sansani na yaki da gwamnatin tsakiya da hambarar da mulkin kasar. Duk matakan da suka dauka sun wuce 'yancin yin magana karkashin tsarin mulkin kasa da babbar doka ta yankin musamman, babu shakka, za a hukunta su yadda ya kamata. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China