Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sassa daban-daban suna goyon bayan daina nuna karfin tuwo, da dawo da kwanciyar hankali a Hong Kong
2019-08-19 10:13:27        cri

Sassa daban-daban a duniya, sun bayyana ra'ayin su a kwanan baya, dake mutunta matsayin da gwamnatin kasar Sin ke dauka wajen magance matsalar Hong Kong, da kuma yin Allah wadai da bore da aka tayar, da wasu kasashen waje suka tsoma baki a kai. Kana sun goyi bayan gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da 'yan sanda wurin, wajen daukar matakan dakile masu bore yadda ya kamata, don kiyaye kwanciyar hankali da wadatar yankin.

Shugaban kungiyar sa kaimi ga dinkuwar kasar Sin dake Masar Chen Jiannan ya ce, Dukkan 'yan kasar Sin dake Masar na goyon bayan kokarin da gwamnatin Sin da kuma gwamnatin yankin Hongkong ke yi, na kiyaye manufar "kasa daya, tsarin mulki biyu" da ma tabbatar da kwanciyar hankali a yankin, sun kuma jinjinawa 'yan sanda da suke kokarin tabbatar da zaman doka da oda, da kiyaye muradun mazauna Hong Kong.

Chen ya kuma kara da cewa, suna adawa da mummunan yunkurin wasu masu bore da nufin kawo cikas ga tsarin "kasa daya, tsarin mulki biyu", da kawo baraka ga kasar. Ban da wannan kuma, suna nuna rashin jin dadi, da kin yarda sosai kan yadda wasu kasashe da kungiyoyi ke tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China