![]() |
|
2019-08-30 13:35:32 cri |
Dakarun tsaron tekun kasar Libya sun sanar a jiya Alhamis cewa, 'yan ci rani sama da 400 ne suka ceto a yayin wasu ayyukan sintiri da suka gudanar a yammacin gabar tekun kasar.
Jami'an tsaron tekun sun kubutar da 'yan ci rani 403 a ayyukan sintirin da suka gudanar a kwanakin baya-bayan nan, a cewar kakakin dakarun tsaron tekun kasar, Ayob Qassem.
A cewar kakakin, an gudanar da ayyukan sintirin ne a gabar tekun birnin Khoms, mai tazarar kilomita 120 daga gabashin birnin Tripoli.
Qassem ya ce, daga cikin 'yan ci ranin da aka ceto, akwai 'yan kasashe daban daban na Afrika, tuni aka kwashe su zuwa wata cibiyar da aka tanada.(Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China