Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU tayi Allah wadai da yin katsalandan na kasashen waje kan harkokin cikin gidan Libya
2019-07-07 17:12:39        cri
A jiya Asabar kungiyar tarayyar Afrika (AU) tayi Allah wadai da yin shisshigi kan batun zaman lafiya da tsaron Afirka, musamman ta nanata halin da ake ciki a kasar Libya.

Kungiyar ta yi kiran gaggawa kan kasashen ketare, dasu guji yin katsalandan kan harkokin zaman lafiya da tsaron Afrika. Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Asabar bayan taro na baya bayan nan da kwamitin sulhun kungiyar ya gudanar game da halin da ake ciki a Libya da kuma irin mawuyacin halin da 'yan cin rani suka tsinci kansu ciki a Libyan.

"Kwamitin sulhun kungiyar ya bayyana damuwarsa musamman bisa katsalandan na kasashen waje game da harkokin cikin gidan Libya wanda hakan na kara haifar da karuwar yaduwar makamai a tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga, lamarin da ya saba dokokin MDD na haramta shigar da makamai kasar, matakin wani yunkuri ne da aka shirya da gangan da nufin haifar da baraka tsakanin masu ruwa da tsaki a kasar Libyan, lamarin dake mayar da hannun agogo baya a yunkurin warware rikicin kasar ta Libya," in ji sanarwar.

Kwamitin ya kara da cewa, duk wani taimakon da za'a bayar daga ketare dole ne ya dace da yunkurin da kungiyar Afirkar ke jagoranta na neman tattaunawa da cimma daidaito tsakanin masu ruwa da tsaki a Libyan." Idan ba haka ba, kwamitin zai ayyana sunayensu a matsayin wadanda ake zargi da yin kafar ungulu wajen warware wannan matsalar."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China