2019-07-26 10:49:10 cri |
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta yi kiyasin 'yan ci rani 150 sun bata, inda ake fargabar sun mutu, biyo bayan kifewar kwale-kwalensu na katako a gabar ruwan Libya.
Kakakin hukumar Charlie Laxley, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, baya ga 'yan ci ranin 150 da ake fargabar sun mutu a jiya Alhamis, masu tsaron gabar tekun Libyan sun ceto wasu mutane 150.
Saboda yanayin rashin tsaro da rikici, biyo bayan hambarar da mulkin marigayin Muammar Gaddafi a shekarar 2011, Libya ta zama hanyar da dubban 'yan ci rani ke bi domin tsallake tekun Bahar Rum zuwa Turai. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China