Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Libya ta duba yiwuwar rufe cibiyoyin kula da shigi da ficin kasar
2019-07-05 09:27:31        cri
Ministan cikin gidan gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD Fat'hi Bashagha, ya sanar a jiya Alhamis cewa, gwamnatin kasar na duba yiwuwar rufe dukkanin cibiyoyin kula da shigi da ficin kasar sakamakon matsalolin tsaro, bayan wani mummunan hari da aka kaddamar a cibiyar dake gabashin babban birnin kasar Tripoli a kwanan nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da Maria do Valle Ribeiro, mataimakiyar wakilin musamman na MDD dake Libya.

A ranar Talata ne, aka kaddamar da hari kan cibiyar shigi da ficin dake gabashin Tripoli, inda aka hallaka gomman mutane da kuma jikkata wasu.

Gwamnatin tana zargin dakarun 'yan adawa dake da sansaninsu a gabashin kasar da kaddamar da harin, zargin da sojojin suka musanta inda suka mayar da zargin harin kan gwamnatin.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), da hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM) sun bukaci a rufe cibiyoyin kula da shigi da ficin Libya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China