![]() |
|
2019-07-06 15:51:54 cri |
Cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya, kwamitin sulhun ya jaddada bukatar saukaka yanayin da ake ciki a Libya ga bangarorin dake adawa da juna a kasar, sannan ya bukaci su cika alkawarin da suka yi na tsagaita bude wuta. A cewar kwamitin, ba za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a kasar ta Libya ba, idan har ba a bi hanyar siyasa da shawarwari ba.
Kwamitin sulhun mai kunshe da mambobi 15, ya bayyana damuwa matuka kan tsanantar yanayin jin kai a kasar Libya, inda suka bukaci bangarori masu ruwa da tsaki na kasar, su samar da cikakkun damammakin gudanar da aiki ga hukumomi masu kula da ayyukan jin kai. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China