Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Libya ta zargi sojojin adawa da yin garkuwa da 'yar majalisar dokoki
2019-07-19 10:19:39        cri
Gwamnatin kasar Libya dake samun goyon bayan MDD ta zargi dakarun sojojin dake adawa masu sansani a gabashin kasar da laifin yin garkuwa da wata 'yar majalisar wakilan kasar.

Gwamnatin ta dora alhakin mummanan aikin kan sojojin, inda ta bayyana cewa wannan wani yunkuri ne da suke yi na neman haifar da tashin hankali da kuma yunkurin haddasa rikici a tsakanin al'ummomin kasar ta Libya.

Gwamnatin ta bukaci shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Libya (UNSMIL), da sauran hukumomin kasa da kasa da su kai dauki.

UNSMIL ta bayyana damuwa sakamakon bacewar Siham Sergewa, inda ta bukaci hukumomin kasar Libya da su gudanar da bincike game da harin da aka kaddamar a gidan Sergewa, kana a binciko inda ake tsare da ita, sannan ta bukaci a gaggauta sako 'yar majalisar dokokin.

Yankin Benghazi yana karkashin ikon dakarun sojojin dake da sansaninsu a gabashin kasar, yankin da a halin yanzu yake cigaba da fuskantar mumman rikici na hare hare da nufin yakar gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD a yunkurin da sojojin ke yi na neman kwace ikon babban birnin kasar Tripoli. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China