Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Libya dake da sansani a gabashin kasar sun kakkabo jirgin sama marar matuki mallakin gwamnati mai samun goyon bayan MDD
2019-07-22 13:16:36        cri

Dakarun sojojin Libya mai sansani a gabashin kasar ta sanar da kakkabo jirgin sama marar matuki kirar Turkiyya mallakin gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD, a yayin da rikici ke ci gaba da yin kamari tsakanin bangarorin biyu.

Jami'an wanzar da tsaron sojojin sun dakatar da harin jirgin marar matuki kirar Turkiyya mallakar mayakan gwamnatin, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin sojojin ta bayyana.

Rundunar sojojin ta ce, an kakkabo jirgin marar matuki ne a yankin Ain Zara dake kudancin birnin Tripoli.

Dakarun sojojin masu sansani a gabashin Libya, karkashin jagorancin Khalifa Haftar, sun sha kaddamar da hare-haren soji tun daga farkon watan Afrilu da nufin kwace ikon birnin Tripoli daga hannun gwamnati.

Kawo yanzu, yakin da ake gwabzawa ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da dubu daya, kana an jikkata wasu mutanen sama da 5,700, yayin da sama da mutane 120,000 rikicin ya tilastawa ficewa daga gidajensu, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ayyana. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China