Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
NCAA ta ja hankalin kamfanonin jiragen sama da su dauki matakan hana yaduwar Ebola
2019-08-14 13:11:16        cri

Hukumar kula da sufurin jiragen saman Najeriya, ta umarci dukkan kamfanonin jiragen sama dake zirga-zirga a shiyya da ma kasa da kasa, da su dauki matakan sanya ido da suka dace, don ganin cutar ba ta shigo cikin kasar ba.

Mai magana da yawun hukumar ta NCAA, Sam Adurogboye, shi ne ya tabbatar da wannan umarni cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a Legas, cibiyar kasuwancin kasar wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta samu kwafe.

Adurogboye ya ce, tuni aka sanar da dukkan kamfanonin jiragen sama wannan umarni, an kuma bukace su da su kara fadakar da ma'aikatansu kan matakan inganta kula da ma sadarwa da jami'an kula da tashi da saukar jiragen sama, a duk lokacin da aka samu rahoton bullar cutar da ake iya yada ta tsakanin fasinjoji. Haka kuma, idan har aka samu rahoton mutuwar maras lafiya a cikin jiragen, ya kamata su tuntubi cibiyoyin kiwon lafiya dake filayen jirgin sama don samun izni, kafin su shigo da gawar mamacin cikin kasar. Su kuma sanar da hukumar NCAA rahoton duk wata cuta da ta bulla a cikin jirgin da ake zaton ana iya yada ta.

Mutane da dama ne dai suka mutu a lokacin da Ebola ta barke a Najeriya a shekarar 2014, bayan da wani Ba-Amurke dan kasar Laberiya mai suna Patrick Sawyer, ya sauka a filin jiragen saman Legas daga Laberiya, inda ya yada cutar.

MDD ta ayyana barkewar cutar a matsayin matsalar harkar lafiyar jama'a ta gaggawa da ta damu duniya baki daya, biyo bayan sake bullar cutar a jamhuriyar demokiradiyar Congo.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China