Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen SADC za su taimakawa DR Congo yakar Ebola
2019-08-13 11:06:32        cri

Darektan kula da harkokin siyasa, tsaro da zaman lafiya a sakatariyar kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SADC) Jorge Cardoso, ya bayyana cewa, kasashe mambobin kungiyar sun bayyana kudurinsu na hada kai don taimakawa Jamhuriyar Demokuradiyar Congo yakar kwayar cutar Ebola da ta barke a kasar.

Jami'in ya ce, a baya-bayan nan ministocin kiwon lafiya daga kasashe mambobin kungiyar su 16, sun gana, inda suka amince da matakan taimakawa Jamhuriyar Demokuradiyar Congo yakar cutar dake kisa. Shawarwarin taron ministocin, zai taimakawa kokarin da sauran abokan hulda na kasa da kasa ke dauka na ganin bayan cutar, ciki har da hukumar lafiya ta duniya (WHO).

Cardoso ya ce, barkewar cutar ba ta bar kowa ba, yana mai cewa, SADC tana daukar matakan da suka dace, don tabbatar da cewa, kwayar cutar ba ta yadu zuwa sauran kasashe ba.

Ma'aikatar lafiyar Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ta sanar da cewa, wannan ita ce, barkewar Ebola ta biyu mafi girma a duniya da Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ta yi fama da ita, inda sama da mutane 1,800 suka rasa rayukansu, baya ga sama da mutane 2,600 da aka tabbatar sun kamu da cutar, tun lokacin da aka ayyana barkewarta a a ranar 1 watan Agustan shekarar 2018.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China