Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta lashi takobin kara kaimi wajen yaki da cutar Ebola
2019-08-15 13:19:34        cri

Yayin da adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar Ebola ya kai 1,782, tarayyar Afrika AU, ta bukaci a kara hada hannu wajen dakile ci gaba da yaduwar cutar Ebola a jamhuriyar demokradiyyar Congo DRC.

Cikin sanarwar da AU ta kan fitar kowanne wata, ta ce hukumar kula da ayyukanta, ta hannun cibiyar takaitawa da yaki da cututtuka ta Afrika ACDC, na kara karfafa taimakon tunkarar cutar Ebola a DRC da sauran sassan Afrika, biyo bayan ayyana cutar a matsayin wadda ke bukatar daukin gaggawa daga kasa da kasa.

A cewar tarayyar, ya zuwa ranar 27 ga watan Yuli, cutar ta yi sanadin mutuwar mutane 1,782 tun bayan barkewarta, inda jimilar adadin wadanda suka mutu ya kai kaso 67 bisa dari.

Alkaluma daga AU din sun nuna cewa, an samu rahoton mutane 2,659 da suka kamu da cutar ya zuwa ranar 27 ga watan Yuli, daga cikinsu kuma an tabbatar da 2,565 sun kamu, yayin ake tababa kan sauran mutanen 94. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China