Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO:An gwada sabbin magungunan Ebola a DRC
2019-08-14 13:13:26        cri

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar da cewa, sabbin magungunan Ebola biyu da aka gwada a kan masu fama da cutar a Jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) ya nuna cewa, idan aka ba su maganin cikin kwanaki uku da nuna alamar suna dauke da kwayar cutar, akwai tabbaci na sama da kaso 90 cikin 100 za su rayu.

Mai magana da yawun hukumar ta WHO, Christian Lindermeier, ya shaidawa zaman MDD cewa, yankin gabashin kasar DRC dake fama da cutar, ya kasance babban kalubale, tun lokacin da aka ayyana barkewar cutar a matsayin harkar lafiya ta kasa da kasa dake bukatar kulawar gaggawa a ranar 17 ga watan Yulin wannan shekara.

MDD ta bayyana cewa, barkewar cutar ta baya-bayan nan, ita ce ta biyu mafi muni, inda ta halaka sama da mutane 1,800 a DRC a cikin wannan shekara.

A watan Nuwanban shekarar da ta gabata ce dai, aka fara gwajin alluran rigakafin cutar guda hudu, biyu daga cikinsu sun nuna alamar kwakkwayan sakamako a kan ragowar. Bayan samun sakamakon ne, wata hukumar sa-ido mai zaman kanta, ta bayar da shawarar dakatar da gwajin da wuri, a yanzu dukkan masu fama da cutar a DRC za a ba su magungunan biyu.

Yayin da sakamakon suka kasance masu muhimmanci kan yaki da cutar, a hannu guda kuma hukumar lafiya ta duniya, ta bayyana cewa, amfani da alluran rigakafin, da magungunan biyu, za su taimaka wajen kawo karshen cutar.

Ya ce, rigakafi, sanya ido, da kokarin gudanar da bincike, da rashin nuna kyama ga mambobin tawagar yaki da cutar da abokan hulda dake cikin al'umma, za su taimaka wajen kara ceton rayuka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China