Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci a gaggauta tsakaita bude wuta a yankunan da aka samu barkewar annobar Ebola
2019-08-03 15:52:47        cri
Kwamitin sulhun MDD ya fitar da wata sanarwa a jiya Juma'a game da yankunan da aka samu barkewar annobar cutar Ebola na baya bayan nan a jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo (DRC), kwamitin ya bukaci a gaggauta tsagaita bude wuta a yankunan da ake cigaba da fuskantar hare haren kungiyoyin masu dauke da makamai.

A cikin sanarwar, kwamitin sulhun MDDr ya bukaci a hanzarta kai dauki ga cutar Ebolar, saboda annobar za ta iya yaduwa cikin sauri, wanda zai iya shafar kasashen dake makwabtaka da yankunan kasar, lamarin da ake fargabar zai iya haifar da mummunan sakamako game da ayyukan jin kai, kuma zai shafi batun zaman lafiyar yankunan kasar baki daya.

Sanarwar ta kara da cewa, MDDr ta bayyana damuwa matuka game da yanayin tabarbarewar tsaro da ake ciki a yankunan da annobar Ebola ta shafa, musamman saboda yawan hare haren da ake kaiwa jami'an aikin ba da jin kan bil adama, da jami'an kiwon lafiya, wanda hakan yana matukar gurgunta ayyukan jami'an kiwon lafiyar, lamarin da zai kara haddasa yaduwar kwayoyin cutar Ebola a sauran yankunan kasar ta Kongo. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China