Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rwanda da Jamhuriyar Congo sun tsaurara matakan dakile yaduwar Ebola a iyakarsu
2019-08-07 10:17:31        cri

Ministar lafiya ta kasar Rwanda, Diane Gashumba da takwaranta na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Pierre Kangudia, sun gana a jiya Talata, inda suka amince su tsaurara matakan kula da zirga-zirga tsakanin iyakarsu, da nufin hana yaduwar cutar Ebola.

Sanarwar da aka fitar bayan ganawar da ta gudana a yankin Rubavu dake arewa maso yammacin Rwanda, wanda ke kan iyaka da garin Goma na gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta ce kasashen biyu sun kuduri niyyar aiwatar da matakan kariya daga cutar Ebola da kuma sa ido kan shige da fice tsakanin iyakarsu domin rage barazanar yaduwar cutar.

Ministocin biyu sun kuma tattauna kan matakan bai daya na kariya da tunkarar cutar Ebola, ciki har da sa ido.

A watan da ya gabata ne, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ayyana barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a matsayin wanda ke bukatar daukin gaggawa daga kasa da kasa.

Kawo yanzu, barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,700. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China