Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamiin Hong Kong: Yankin ya yi asara sosai saboda dakatar da zirga zirgar jiragen sama
2019-08-13 11:21:31        cri

Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong ta zanta da manema labarai a jiya Litinin, inda shugaban hukuma mai kula da harkokin yankin Zhang Jianzong ya nuna cewa, gwamnatin na yin Allah wadai da aikin nuna karfin tuwo da kakkausar murya, da kuma goyon bayan matakin da 'yan sanda suka dauka, yadda ya kamata. Zhang ya kara da cewa, yanzu Hong Kong na fuskantar hali mai hadari, kila ci gaban da yankin ke samu cikin shekaru da dama zai lalace. Ya kuma yi kira ga mazauna da su zama masu kaunar Hong Kong duk da matsayin da suka dauka, sannan ba wanda zai iya keta doka da tada tarzoma don cimma burinsa.

Shugaban hukumar kula da zirga-zirga da gidaje na yankin Chen Fan ya ce, an yi taro ba tare da samun izni ba a wannan rana a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na yankin Hong Kong, inda masu zanga-zanga suka haifar da cikas ga ayyuka zirga-zirga da maganar bayyana ra'ayoyinsu, matakin da ya dakatar da ayyukan zirga-zirga, kuma ya haifar da asara matuka. Ya kuma jaddada cewa, Hong Kong mahada ce ta zirga-zirgar jiragen sama da ya kai matsayi na uku a duniya wajen jigilar fasinjoji, yawan fasinjoji da suke ratsa Hong Kong a ko wace rana ya kai fiye da dubu 200, zanga-zangar da aka gudanar a wannan karo ya yi illa ga zaman rayuwar mazauna fiye da dubu 800 wadanda ayyukansu ke da alaka da zirga-zirgar jiragen sama.

A nasa bangaren, shugaban hukumar tsaro ta yankin Li Jiachao ya ce, masu tarzoma sun kai hari 'yan sanda da daukar wasu mumunan matakai, ciki hadda bom din da aka hada da fetur, kayayyakin harbe-karbe, duwatsu na karafa da dai sauransu. Ban da wanann kuma, 'yan sanda sun gano wasu kayayyakin hada bom da bom da aka hada, da hayaki mai sa kwalla da wuka da dai sauran makamai masu karfi. Wadannan ayyukan bore za su kawo babbar illa kuma suna tsorantar da mutane kwarai da gaske. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China