Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta shafe shekaru 3 ba tare da samun rahoton bullar cutar polio ba
2019-08-22 11:20:50        cri

Najeriya ta sanar da cewa shekaru uku ke nan a jere ba'a samu wani rahoton bullar kwayar cutar shan-inna ko kuma polio ba, inda mahukuntan kasar suka bayyana cewa Najeriyar ta shirya tsaf wajen kafa tarihin zama kasar da ta yi ban kwana da cutar polio.

Rahoton bullar kwayar cutar polio na karshe da aka samu a kasar shi ne na watan Agustan shekarar 2016 a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Hukumomin lafiyar Najeriya sun bayyana cewa an fara shirye-shiryen tabbatar da ayyana kasar a matsayin wacce ta kawar da cutar shan inna baki daya, wanda ake sa ran ayyanawa a watan Maris na shekarar 2020, matukar dai al'amurra ba su sauya ba.

Shugban hukumar kula da lafiya a matakin farko na kasar (NPHCDA) Faisal Shuaib, ya bayyanawa 'yan jaridu a Abuja cewa, baya ga makudan kudaden da ake warewa ga shirin yaki da cutar polio a cikin kankanin lokaci daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnatin tana kuma ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran bangarorin kasa da kasa dake tallafawa shirin.

Wakiliyar hukumar tallafawa ilmin kananan yara ta MDD UNICEF dake Najeriya, Pernille Ironside, ta bayyana nasarar da cewa babban ci gaba ne ga kyautatuwar rayuwar dukkan yara a fadin Najeriya. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China