Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya: mutane 4 sun mutu sakamakon harin da aka kaiwa ayarin motocin mataimakin gwamnan Nasarawa
2019-08-22 10:46:11        cri
'Yan sandan Nijeriya sun bayyana a jiya Laraba cewa, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun kai hari kan ayarin motocin mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Emmanuel Akabe, lamarin da ya yi sanaddiyar mutuwar 'yan sanda 3 da wani direba. Emmanuel Akabe ya tsallake harin lami lafiya, kuma 'yan sanda na kokarin cafke wadanda suka aikata wannan ta'asa.

An ba da labarin cewa, harin ya auku ne a daren ranar 20 ga wata, lokacin da Akabe ke kan hanyar sa ta zuwa Abuja, fadar mulkin kasar, inda 'yan bindigar suka bullo ta yankin kan iyakar jihar Nasarawa, suka kuma bude wuta kan ayarin motocin, lamarin da ya haifar da musayar wuta da 'yan sandan dake cikin ayarin, kafin daga bisani maharan su tsere. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China