Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya rantsar da sabuwar majalisar ministocin kasar
2019-08-22 10:49:14        cri

A jiya Laraba shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da sabuwar majalisar zartaswar kasar a karo na biyu na wa'adin shugabncinsa, inda ya sake baiwa kansa mukamin ministan albarkatun man fetur.

Shugaba Buhari, wanda ya rike wannan mukami na tsawon shekaru 4 a wa'adin mulkinsa na farko, majalisar ta kunshi adadin ministoci 43, daga cikinsu mata 8 kacal aka baiwa mukamin ministocin, kana an sake nada sakataren gwamnatin tarayyar kasar tare da ba su rantsuwar kama aiki wanda aka gudanar a fadar shugaban kasar dake Abuja, babban birnin kasar.

An raba ma'aikatar kula da sufurin jiragen sama daga ma'aiktar sufuri, yayin da ma'aikatar lantarki aka raba ta daga ma'aikatar lantarki, ayyuka da gidaje.

Shugaban kasar ya bukaci sabuwar majalisar ministocin kasar da ta yi aiki tukuru domin daga matsayin ci gaban kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika zuwa mataki na gaba, yana mai cewa, manyan manufofin wannan gwamnati sun hada da inganta tsaro, fadada hanyoyin bunkasa tattalin arzikin kasar, da yaki da rashawa.

A cewar shugaban kasar, ya gamsu za'a iya gina ingantaccen yanayin ci gaban tattalin arziki wanda zai samar da kyakkyawan yanayi ga makomar rayuwar dukkan jama'ar kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China