Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Huawei ya horas da ma'aikatan Najeriya dabarun tafiyar da harkokin gwamnati ta Intanet
2019-08-23 20:43:58        cri

Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya, ta kara haifar da kyakkyawan sakamako, yayin da katafaren kamfanin sadarwa na kasar Sin Huawei ya kammala horas da ma'aikata 935 daga Najeriya, dabarun fasahar sadarwar zamani.

Shirin horon mai taken "sauyi karkashin fasahar sadarwar zamani", an fara shi ne a watan Janairu aka kuma kammala a watan Yunin wannan shekara, an kuma gudanar da horon ne cikin rukunoni 19. Manufar horon dai ita ce, horas da ma'aikatan kasar ta Najeriya dabarun fasahar sadarwar zamani da inganta harkokin gwamnati ta intanet.

An dai tsamo mahalarta shirin ne daga ma'aikatu da hukumomin tarayyar kasar daban-daban, bayan da gwamnatin tarayyar Najeriya da kamfanin na Huawei suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a watan Oktoban da ya gabata.

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha, ya bayyana shirin a matsayin daya daga cikin alamun dake kara karfafa alaka tsakanin gwamnati da sassa masu zaman kansu a Najeriya. Shi ma ministan sadarwar najeriya, Ali Isa Pantami, ya ce shirin samun horon, ya zama wajibi ga ma'aikatan, ta hake ne za su inganta kwarewarsu domin fuskantar kalubalen dake gaba.

Ma'aikatan da suka ci gajiyar shirin, sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, suna alfahari da kasancewa cikin ma'aikatan da suka ji gajiyar shirin, kuma za su yi kokarin ganin kasar ta cimma burinta a fannin fasahar zamani, ta hanyar daina amfani da takarda a nan gaba, inda za a rika amfani da fasahar zamani, wajen adana muhimman bayanai, kamar yadda kasar ke fatan cimma wannan buri.

A jawabinsa jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya bayyana cewa, kokarin gwamnatin Najeriya na yin hadin gwiwa da kamfanin Huawei domin kara kwarewar ma'aikatanta, yana daya daga cikin manyan manufofi 8 na bunkasa alaka tsakanin Sin da Afirka da aka sanar a taron kolin na FOCAC na Beijing da ya gudana a watan Satumban da ya gabata.

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na karfafa musaya da hadin gwiwa da hukumomin kasashen biyu, da musayar kwarewa a fannin fasahar sadarwar zamani.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China