Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta musanta zargin Amurka, tana mai cewa matakanta na soji na kare kai ne
2019-08-06 11:15:45        cri

Kasar Sin ta yi watsi da ikirarin da Sakataren tsaron Amurka ya yi a baya-bayan nan cewa, Sin na kokarin durkusar da yankin kewayen tekun Indiya da Fasifik, tana mai cewa ire-iren kalaman na kokarin shafa mata kashin kaji a wani yanayi da bai dace ba, kuma matakanta na soji, na kare kai ne.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ne ta bayyana haka a jiya, lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai.

Hua Chunying ta ce Amurka ta dauki wani lokaci na fakewa da kasar Sin game da batun amfani da makamai masu linzami dake cin gajere da matsakaicin zango da sauran batutuwa, tana mai zuzuta abun da take kira 'barazanar makaman nukiliyar kasar Sin' ba tare da tushe ba. Kakakin ta ce wannan shi ne abun da Amurka ke yi, wato dorawa wasu kasashe laifi. Har ila yau, ta ce duk da adawar da kasashen duniya suka nuna, Amurka ta zabi janyewa daga yarjejeniyar haramta amfani da makamai masu linzami dake cin gajere da matsakaicin zango, kuma a yanzu tana neman girkesu a yankin Asiya.

Ta ce dukkan makamai masu linzami dake cin gajere da matsakaicin zango na kasar Sin na cikin iyakokinta, wanda kuma ya nuna yanayin manufar tsaron kare kai ta kasar.

Hua Chunying ta ce kasar Sin ba za ta nade hannu tana kallo ana illata muradunta ba. Ta ce ba kuma za ta kyale wata kasa ta kawo mata matsala har iyakarta ba, don haka za ta dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen kare muradunta na tsaron kasa.

Ta ce ana fatan Amurka za ta rika tabbatar da gaskiya da kauracewa ta'azzara zaman dar-dar ko illata zaman lafiyar kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China