Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu ci gaba game da cinikayyar amfanin gona tsakanin Sin da Amurka
2019-07-29 10:45:23        cri

A ci gaba na baya-bayan nan da aka samu game da cinikayyar amfanin gona tsakanin kasar Sin da kasar Amurka tun bayan ganawar shugabanin kasashen biyu a birnin Osaka na Japan a watan Yuni, an turo miliyoyin ton na waken soyar Amurka zuwa kasar Sin.

Haka kuma, Amurka ta sanar da cire karin haraji kan kayayyaki 110 na kasar Sin, sannan ta bayyana shirinta na ci gaba da ba 'yan kasuwarta damar samar da kayayyaki ga takwarorinsu na kasar Sin.

A cewar majiyoyi daga hukumar raya kasa da aiwatar da gyare-gyare ta kasar Sin da ma'aikatar kasuwancin kasar, wannan ya nuna cewa, a shirye bangarorin biyu suke su aiwatar da matsayar da shugabanin kasashen suka cimma a Osaka.

Tun daga ranar 19 ga watan nan, wasu kamfanonin kasar Sin suka fara tuntubar masu samar musu da kayayyaki a Amurka, game da sayen amfanin gona daga kasar, ciki har da waken soya da auduga da naman alade da dawa. A yanzu haka, an cimma yarjejeniyoyi bisa sharuddan da kasuwa ta tanada.

Majiyoyi daga sassan gwamnatin kasar Sin masu alaka da batun, sun ce ya kamata bangaren Amurka ya dauki managartan matakan cika alkawurran da ya dauka tare da samar da yanayi mai kyau na tattauna batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin biyu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China