Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya Kamata A Dauki Mataki Mai Dacewa Don Mayar Da Martani Kan Matakan Kariyar Ciniki na Amurka
2019-08-24 16:19:31        cri
Game da matakin da gwamnatin kasar Amurka ta dauka na kara sanya haraji da ya kai kaso 10% kan wasu kayayyakin da take shigo da su daga kasar Sin wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 300, kasar Sin a jiya Juma'a ta da sanya harajin da ya kai kaso 10% da kaso 5% a kan wasu kayayyakin Amurkar da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 75 da take shigo da su daga kasar ta Amurka, kuma matakin zai fara aiki ne kan rukuni na farko na kayayyakin daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, kana daga ranar 15 ga watan Disamba matakin zai fara aiki kan rukuni na biyu na kayayyakin.

Har wa yau, tun daga ranar 15 ga watan Disamban bana, za ta maido da harajin da ya kai kaso 25% da kaso 5% a kan motoci da kayan gyaran motoci da take shigo da su daga kasar.

Kasar Sin ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martani kan matakan kariyar ciniki da Amurka ke dauka. Matakin da Sin ke dauka yana mai dacewa, wanda kuma ya shaida cewa, babu amfanin da aka samu wajen yin matsin lamba ga kasar Sin, Sin za ta cika alkawarinta na mayar da martani. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China