Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu jagorantar shawarwarin tattalin arziki da ciniki tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka sun tattauna
2019-08-14 11:03:04        cri

Mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin kana mataimakin firaministan kasar Sin, kuma mai kula da shawarwarin tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Amurka Liu He ya kira wakilin ciniki na Amurka Robert Lighthizer da ministan kudin Amurka Steven Mnuchin ta wayar tarho a daren jiya Talata. Inda Sin ta nuna rashin jin dadinta kan shirin da Amurka ta yi na kara sanyawa kayayyakinta dake shiga Amurka haraji, daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, kuma bangarorin biyu sun kai ga matsaya daya na sake bugawa juna waya a makonni biyu masu zuwa. Ministan kasuwancin kasar Sin Zhong Shan, shugaban bankin jama'ar kasar Sin Yi Gang, da kuma mataimakin direktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima Ning Jizhe sun shiga tattaunawar ta wannan karo. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China