2019-08-15 20:18:15 cri |
Wani jami'in ofishin hukumar kwastam sashen haraji na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya ce mahukuntan Sin sun dauki dukkanin matakan da suka wajaba, domin mayar da martani ga kudurin gwamnatin Amurka, na buga karin haraji kan hajojin Sin da ake shigarwa Amurka.
Gwamnatin Amurka dai ta ayyana buga karin harajin kaso 10 bisa dari, kan wadannan hajoji na Sin da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 300.
Kasar Sin ba ta da wani zabi, illa daukar wannan mataki na mayar da martani. Kuma matakin Amurka ya saba wa matsaya daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma a shawarwarin da suka yi a kasar Argentina da kuma a birnin Osaka na kasar Japan.
A maimakon daidaita batutuwa masu nasaba da wannan takaddama ta hanyar tattaunawa, Amurka ta sake daukar matakin kara dora haraji, inda ya kaucewa madaidaiciyar hanyar warware batutuwan. Ko da yake Amurka ta ce za ta dakatar da kara dora kudin haraji kan wasu kayayyakin da kasar Sin ke sayarwa a Amurka, amma muddin ba ta soke matakinta ba, to kuwa tabbas hakan zai illata moriyar kasar Sin. Don haka daidai ne ita ma kasar Sin ta shirya daukar matakai.
Sanin kowa ne cewa, babu wanda zai ci nasara a yakin ciniki. Kaza lika tsanantar takaddamar ciniki za ta kawo illa ga kasashen Sin da Amurka, da ma duk duniya baki daya. Kasar Sin tana son daidaita batutuwan ta hanyar yin hadin gwiwa, amma akwai ka'idoji. Har wa yau kasar Sin ba za ta ja da baya kan manyan al'amura ba. Ko da yake Sin ba ta son yin yakin ciniki, amma fa ba ta tsoronsa muddin ya zama wajibi.
Har kullum kasar Sin ba za ta sauya manufarta ba. Wato dai idan ana bukatar tattaunawa, Sin za ta tattauna, kana idan ana son yin yakin ciniki, Sin za ta shiga fagen yaki. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China