Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban Kenya 182 da suka samu tallafin karatu na gwamnatin kasar Sin za su tashi zuwa kasar
2019-08-28 10:47:05        cri
A jiya Talata, ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya, ya gudanar da bikin ban kwana da daliban kasar ta Kenya 182 da suka samu tallafin karatu na gwamnatin kasar Sin na shekarar 2019, wadanda za su tashi zuwa kasar Sin domin kara ilmi.

A jawabin da ya gabatar, karamin jakadan kasar Sin a kasar ta Kenya, Zhao Xiyuan, ya ce, a bana ake cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, kuma a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, Sin ta yi iyakacin kokarin raya harkokin kimiyya da ba da ilmi, matakin da ya gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin da zaman al'umma. Ya kara da cewa, Sin da Kenya sun kara hadin kansu a fannoni daban-daban domin tabbatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Jakadan ya ce tun daga lokacin da kasar Sin ta fara baiwa kasar Kenya irin wannan tallafin karatu a shekarar 1982, ya zuwa yauzu, dalibai fiye da 2400 sun kara ilminsu ta hanyoyin daban-daban a kasar Sin.

Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Kenya, Raila Amollo Odinga, ya yabawa goyon baya da taimakon da Sin take baiwa kasar a fannin ba da ilmi.

A nasa bangaren, wakilin daliban ya ce, yana sa ran kara ilminsa a kasar Sin, kuma zai yi iyakacin kokarinsa wajen yin karatu don yin amfani da wannan zarafi mai kyau. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China