Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Kenya sun tsaurara matakan yaki da fataucin muggan kwayoyi
2019-08-26 10:29:40        cri
Wata jami'ar 'yan sanda mace tana daya daga cikin mutane 7 da aka damke a birnin Mombasa na gabar tekun kasar Kenya bisa zarginsu da hannu a fataucin kokin da kwayar heroin mai bugarwa a ci gaba da yakin da ake da masu fataucin muggan kwayoyin a fadin kasar, hukumar 'yan sandan kasar Kenya ne ta ayyana hakan a ranar Lahadi.

Hamdi Yusuf Maalim, wacce ke aiki a ofishin 'yan sanda na Likoni, an damke ta tare da takwarorinta a yankin Diani, dake tekun kudancin kasar a ranar Juma'a.

Jami'in dake kula da shiyyar tekun kasar Kenya, John Elungata, ya fadawa manema labaru a Mombasa cewa, akwai jerin sunayen mutane da dama da ake zargi, kuma ya yi amanna za su damke su muddin suka ki mika wuya. Ya ce sun samu labarin wasu daga cikinsu sun tsere zuwa Tanzania da sauran wurare amma suna ci gaba da bibiyarsu, koda kuwa wadanda ake zargin ma'aikatan gwamnati ne.

Elungata ya ce, ya kamata a hada karfi da karfe wajen kakkabe ayyukan manyan dillalan dake fataucin muggan kwayoyin a biranen kasar. Ya ce an shigar da matasa da dama cikin bada-kalar ta'ammali da muggan kwayoyi kuma ba za su laminta matsalar ta ci gaba ba.

A cewarsa, sauran mutanen da 'yan sanda ke farautarsu sun hada da wasu ma'aikatan filin jirgin saman kasa da kasa na Moi, da hukumar kula da tashoshin ruwan Kenya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China