Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya tana mai sabunta alkawarin karfafa kare yara
2019-06-17 10:29:59        cri
Kenya ta gudanar da bikin ranar Yaran Afrika a jiya Lahadi, inda ta sabunta alwashinta na karfafa kare yara daga cin zarafi da bauta da kuma watsi da ake da su.

Sanarwar da sakataren gwamnati dake kula da harkokin kwadago da kare al'umma, Ukur Yatani ya fitar, ta ce gwamnati ta jajirce wajen inganta walwalar yara, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Yana mai cewa gwamnati na ci gaba da amfani da ka'idar "hakkin yara gaba da komai" musammam hakkin rayuwa da samun ci gaba da tabbatar da daidato a tsakaninsu.

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin Afrika da hukumomin da kungiyoyin al'umma, su ba batun kare yara daga hadduran da suka jibani ayyukan dan Adam da annoba daga Allah muhimmanci.

Taken ranar Yaran Afirka na bana shi ne; "ayyukan jin kai a Afrika: hakkin yara gaba da komai" wanda ke da nufin kira ga gwamnatoci da al'ummomi su jajircewa wajen inganta walwalar yara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China