Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya ya kaddamar da gasar kasuwanci ta matasa a Kenya
2019-07-10 19:52:53        cri
Darektan bankin duniya mai kula da kasashen Eritrea da Kenya da Rwanda da Uganda, Carlos Felipe Jaramillo, ya bayyana cewa, bankin ya kaddamar da gasar kasuwanci ta matasa a kasar Kenya, a wani mataki na magance matsalar rashin aikin yi.

Jami'in bankin ya shaidawa manema labarai a birnin Nairobin kasar Kenya cewa, bankin ya ware kudin kasar Kenya Shillings biliyan 1.38 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 13.5 don shirya wannan gasa mai suna MbelenaBiz, wadda za ta tallafawa matasa 750.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China