Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban sakataren jamiyyar Jubilee ta Kenya: Amurka ta lalata tsarin ciniki na duniya
2019-06-20 10:33:06        cri

Babban sakataren jam'iyyar Jubilee dake kan karagar mulkin kasar Kenya Raphael Tuju ya bayyanawa 'yan jaridan kasar Sin a birnin Nairobi a kwanakin baya cewa, Amurka ta tsananta takaddamar ciniki a tsakaninta da kasar Sin, matakin wanda zai kawo babbar illa ga tsarin ciniki na duniya da tattalin arzikin duniya, ya kamata bangarorin biyu su daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwari.

Tuju ya bayyana cewa, kasarsa ta Kenya ta nuna goyon baya ga tsarin raya duniya na bai daya da ra'ayin bangarori daban daban. Game da takardar matsayin Sin dangane da shawarwarin dake tsakanin Sin da Amurka kan tattalin arziki da cinikayya, Tuju ya bayyana cewa, takardar ta shaida matsayin Sin kan daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwarin, gwamnatin kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan gudanar da ayyukan bisa ka'idoji. Ya yi kira ga bangarorin Sin da Amurka su yi hadin gwiwa da neman hanyoyi masu dacewa wajen daidaita matsalarsu yadda ya kamata.

Tuju ya ce, a cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin ta bunkasa daga kasa mafi samun karancin ci gaba zuwa kasa ta biyu mafi ci gaban tattalin arziki a duniya, kana ta kawar da talauci ga mutane fiye da miliyan 100, wannan babbar nasara ce da dan Adam ke samu a tarihi. Tsarin bunkasuwar kasar Sin yana da babbar ma'ana ga kasashen duniya da dama. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China