Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya za ta fitar da ganga 400,000 na danyen mai a bana
2019-08-21 10:02:28        cri
Kasar Kenya na sa ran fitar da ganga 400,000 na danyen mai a bana, inda za ta kasance kasa ta farko a gabashin Afrika da ta fara fitar da mai zuwa kasuwar duniya.

Babban Sakataren ma'aikatar man fetur da hakar ma'adinai, Andrew Kamau, ya shaidawa manema labarai a Nairobi cewa, ana gudanar da cinikin man ne karkashin shirin EOPS, mai jigila da tace danyen mai a matakin farko na fara samar da shi, wanda kuma ke neman samarwa man kasuwa.

Andrew Kamau, ya ce za a fitar da kashin farko na ganga 200,000 a rubu'i na 3 na bana, inda za a sayar da kashi na biyu zuwa karshen shekara. Yana mai cewa za a sayar da galibin man ne a nahiyar Asia.

Ya ce karkashin shirin EOPS, wanda ake gudanarwa bisa hadin gwiwar kamfanonin mai na Tullow da Afrika da Total, kasar za ta rika samar da ganga 2,000 na mai a kullum daga rijiyoyin mai dake arewa maso yammacin kasar.

Kenya ta gano rijiyoyin mai ne a shekarar 2012 wanda a yanzu aka yi kiyasin sun kai ganga miliyan 750. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China