Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta kaddamar da cibiyar horo kan inganta moriyar tattalin arzikin teku
2019-07-09 10:42:39        cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya kaddamar da cibiyar horo kan inganta tattalin arzikin albarkatun teku a birnin Mombasa dake bakin teku, a wani mataki na aiwatar da sauyi, wanda zai bunkasa nasarorin da mahukuntan kasar ke fatan samu.

An dai dorawa cibiyar ta Bandari Maritime, nauyin magance karancin kwararru a fannin sufurin ruwa a Kenya, da ma yankin da kasar take, ta yadda hakan zai dace da matakan fadada raya tattalin arzikin teku.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da cibiyar a jiya Litinin, shugaba Kenyatta, ya ce sauye-sauye da gwamnatinsa ke aiwatarwa, na da nufin samar da matasa kwararru, wadanda za su yi aiki a fannin sufurin ruwa a cikin kasar, da ma tsakanin manyan ruwayen kasa da kasa.

An yi hasashen cewa, idan an yi kyakkyawan amfani da wannan sashe na tattalin arzikin teku a kasar Kenya, za a iya cin gajiyar da ta kai kudin kasar Shillings biliyan 380, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 4.8, kana sashen zai iya samar da ayyukan yi sama da 52,000 a tsawon shekaru 10 masu zuwa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China