Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rufe gasar fasahar sanaoi ta kasa da kasa karo na 45
2019-08-28 10:30:26        cri

An rufe gasar fasahar sana'o'i ta kasa da kasa karo na 45, a jiya Talata a Kazan na kasar Rasha. Tawagar Sin ta kai matsayin farko a fannonin samun lambobin yabo na zinari da adadin lambobin yabo da kuma samun makin kungiya-kungiya.

Ana gudanar da irin wannan gasa ne a shekaru biyu biyu, inda ta kasance gasa mafi girma kuma mafi samun karbuwa da ta kai matsayin farko a duniya, har an yi mata lakabin "Gasar fasahar sana'o'i irin na Olympic". Gasar tana bayyana bunkasuwar fasahar sana'o'i dake kan gaba a duniya, kuma ta zama wani muhimmin dandali na nuna da kuma musanyar fasahohi tsakanin mambobin kungiyar fasahar sana'o'i ta kasa da kasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China