Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Haduwar Trump da Putin ta bada kwarin gwiwa game da kyautata dangantakar kasashensu
2019-07-02 11:00:13        cri
Mataimakin Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov, ya ce haduwar Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump ta baya-bayan nan, ta bada kwarin gwiwa, sai dai yanayin cikin gidan Amurka na iya hana farfado da dangantakar kasashen biyu da wuri.

Yayin wani taron kungiyar tattauna muhimman batutuwan kasa da kasa ta Valdai, Sergei Ryabkov, ya jaddada cewa, haduwar shugabannin biyu a birnin Osaka, ta samar da dandalin yi wa makomar dangantakar kasashen kyakkyawan fata, duk da tarin wasu batutuwa dake akwai.

Da yake tsokaci kan ganawar da shugabannin biyu suka yi Juma'ar da ta gabata, a gefen taron kungiyar G20 da ya gudana a Osakan kasar Japan, Jami'in ya ce, la'akari da yadda ake samun kalaman kiyayyar Rasha a tsakanin 'yan bokon Amurka, ciki har da majalisar dokokin kasar, zai yi wuya a sa ran samun ci gaba game da dangantakar bangarorin biyu.

Ryabkov ya ce bangaren Rasha ta nuna sha'awarta na daukaka dangantakar, yana mai cewa yanzu komai ya dogara ne akan shugabancin Amurka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China