Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Putin: Matakin kasashen yammacin duniya na hana bunkasuwar 'yan takararsu ba shi da makoma
2019-07-10 13:51:53        cri

Shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin ya bayyana a birnin Ekaterinburg dake tsakiyar kasar Rasha a jiya cewa, a yayin da ake kokarin raya duniya bisa tsarin bai daya, matakin da kasashen yammacin duniya ke dauka na hana bunkasuwar abokan hamayyarsu ba zai yi tasiri ba.

Putin ya bayyana a yayin da yake zantawa da daliban jami'ar tarayya ta Ural a wannan rana cewa, yayin da suke adawa da abokan hamayyarsu a duniya, kasashen yammacin duniya ba su inganta karfinsu a duniya ba, amma sun hana bunkasuwar abokan adawar tasu, wannan mataki ba shi da makoma.

Putin ya kara da cewa, ya ji mamaki da matakin kasar Amurka na saka takunkumi ga kamfanin Huawei da hana daliban kasar Sin su yi karatu a wasu sassan jami'o'in kasar. Abun da Amurka ba ta fahimta ba, shi ne a yayin da ake kokarin raya duniya bisa tsarin bai daya, ba a iya rufe kofa ga kasashen waje, ilmi da kimiyya da fasaha za su bunkasa a kasashe masu tasowa, babu shakka kuma wasu kasashe za su samu ci gaba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China