Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Putin: Rasha na son bunkasa hulda da Amurka
2019-06-24 14:57:27        cri
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a jiya Lahadi ya bayyana cewa, kasarsa na son bunkasa huldar dake tsakaninta da Amurka, kuma su yi kokarin cimma daidaito ta hanyar yin shawarwari.

A yayin da yake karbar intabiyun da NTV na kasar ya yi masa, ya ce, Rasha da Amurka nada matsaya mabanbamta a kan wasu harkokin duniya, sai dai gwamnatin Amurka ta gane cewa, Rashan ba zata mika wuya ba a sakamakon yadda aka matsa mata lamba, don haka, ya zama dole kasashen biyu su yi shawarwari da juna.

Mr.Putin ya jaddada cewa, idan Amurka na bukatar yin shawarwari, to, Rasha a shirye take, idan kuma Amurkar bata so, lalle Rasha zata ci gaba da jira har zuwa lokacin da Amurka ta shirya.

Putin ya kara da cewa, shugaba Trump na iya yanke shawara kan manufofin diplomasiyya na kasar, sai dai tsarin kasar ta Amurka ya yi masa tarnaki, abin da yasa ya kasa wajen gudanar da ayyuka da yawa da yake son aiwatarwa.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China