Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Putin: An tsananta dangantakar dake tsakanin Rasha da Amurka
2019-06-14 11:18:14        cri
An gabatar da bidiyo game da hirar da aka yi da shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin a shafin Intanet na fadar shugaban kasar Rasha, inda ya bayyana cewa, an tsananta dangantakar dake tsakanin Rasha da Amurka.

Putin ya bayyana a cikin bidiyon cewa, dangantakar dake tsakanin Rasha da Amurka ta samu koma baya. Ya ce, a cikin wasu shekaru da suka gabata, gwamnatin kasar Amurka a wannan karo ta tsai da kudurori fiye da 10 na sakawa Rasha takunkumi.

Putin ya jaddada cewa, duk wani aikin lalata tsarin dangantakar tattalin arziki a tsakanin kasa da kasa dake kasancewa a dogon lokaci zai kawo illa ga bangarori daban daban da suka gudanar da ayyukan tattalin arziki. Kana yana fatan dukkan kasashen abokan huldar kasar Rasha ciki har da kasar Amurka za su tsaida kuduri kan batun tattalin arzikin duniya a yayin taron koli na kungiyar G20 da za a gudanar a karshen wannan wata, hakan zai samar da sharadi ga hadin gwiwar tattalin arziki a tsakaninsu.

A sakamakon batun kasar Ukraine, da batun sanya guba ga tsohon mai leken asiri na Rasha, da yadda Amurka da Rasha suka dakatar da aiwatar da yarjejeniyar lalata makamai masu linzami na matsakaici da gajeren zango na kasashen biyu da sauransu, an tsananta dangantakar dake tsakaninsu a shekarun baya baya nan. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China