Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Rasha da Amurka za su gana a wajen taron kolin G20
2019-06-27 10:32:22        cri
Mashawarcin shugaban kasar Rasha kan manufofin diflomasiyya Yuri Ushakov ya ce, shugaba Vladimir Putin da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump za su yi shawarwari a wajen taron kolin kungiyar kasashen G20 a gobe Jumma'a a birnin Osakar kasar Japan, inda za su tattauna kan batutuwan da suka shafi dangantakar kasashen biyu da na sauran yankuna.

Yuri ya ce, bisa jadawalin da aka tsara, batutuwan da za su tattauna sun hada da, dangantakar kasashen Rasha da Amurka, da zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da rikice-rikicen da suka wakana a wasu kasashen yankin, ciki har da Syria, Afghanistan, Ukraine, Venezuela da sauransu.

Har wa yau, shugabannin biyu za su mai da hankali kan halin da ake ciki a kasar Syria gami da ayyukan hadin-gwiwa da kasashen Rasha da Amurka suke yi na tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China