Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin Hongkong ta yi Allah wadai da aikace-aikacen nuna karfin tuwo
2019-08-11 15:50:49        cri
Kakakin gwamnatin yankin musamman na Hongkong na kasar Sin ya furta a jiya Asabar cewa, an yi haramtacciyar zanga-zanga a wasu unguwannin yankin a jiya, inda masu zanga-zangar suka lalata wasu kayayyakin jama'a, da toshe manyan hanyoyi, ciki har da wani bututun karkashin teku mai dauke da hanyar mota, lamarin da ya haddasa cunkuson motoci mafi tsanani, da haifar da mummunan tasiri ga harkokin kasuwanci. Ban da haka kuma, wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi ta kunna wuta a wasu wurare daban daban, abin da ya zama hadari ga tsaron jama'a. Saboda haka, gwamnatin yankin Hongkong ta yi Allah wadai da yadda ake aikace-aikacen nuna karfin tuwo, ba tare da lura da ka'idoji da bukatun sauran mutane ba.

Kakakin ya kara da cewa, sakamakon haramtacciyar zanga-zangar, a kowace rana a kan rufe wuraren samar da hidimomi ga jama'a kafin lokacin da aka kayyade, don tabbatar da tsaron jama'a, lamarin da ke addabar zaman rayuwar mazauna yankin Hongkong.

Kakakin ya nanata cewa, 'yan sandan Hongkong za su yi kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu, don gurfanar da mutanen da suka keta doka a gaban kuliya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China