Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin yankin musamman na Hongkong ta yi Allah wadai da zanga-zangar dake faruwa a yankin
2019-08-12 15:13:29        cri

Mai magana da yawun gwamnatin yankin musamman na Hongkong ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan zanga-zangar nuna karfin tuwo da aka gudanar jiya Lahadi.

Ya ce, baya ga zanga-zangar da aka gudanar ba bisa doka ba ranar 10 ga wata a Kowloon da New Territories, an sake shirya wasu gangami ba bisa doka ba a wurare daban-daban a Hongkong, inda masu zanga-zangar suka lalata kayayyakin gwamnati tare da toshe hanyoyi. Sun kuma toshe ofisoshin 'yan sanda da kaiwa 'yan sanda hari da hasken laser da tubali. Wasu masu zanga-zanga sun jefi 'yan sanda da bam din da aka hada da fetur har suka raunata jami'an 'yan sanda.

Wadannan matakai na karya doka da masu zanga-zangar suka dauka sun haifar da babbar barazana ga tsaron lafiyar 'yan sanda da mazauna wurin, gwamnatin yankin na nuna matukar rashin jin dadi da bacin rai kan lamari tare da yin Allah wadai da shi da kakaussar murya.

Ya kara da cewa, zanga-zangar da aka gudanar jiya Lahadi ba bisa doka ba, ta sa an rufe manyan ababen ba da hidimma ga jama'a da wuri. Wadannan ayyukan nuna karfin tuwo da aka dade ana yi sun karya doka, tare da kawo illa ga wurare da yawa, sun kuma keta hakkin yawancin jama'ar wurin. Hakan ya sa, gwamnatin yankin ke yin kira ga jama'a da su bayyana rashin amincewarsu da tashin hankali kana su taimakawa al'umma wajen gaggauta dawo da doka da oda a yankin.

Haka kuma wajibi ne 'yan sandan yanki za su tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata, ta yadda za a hukunta masu zanga zangar nuna karfin tuwo. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China