Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta baiwa dalibai 'yan Nijeriya 58 kyautar kudin karatu na shekarar 2019/2020
2019-08-08 13:53:10        cri
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya ya gabatarwa dalibai 'yan Nijeriya 58 kyautar kudin karatu na gwamnatin kasar Sin na shekarar 2019/2020 a jiya Talata, tare da ba su takardar sanar da daukar dalibai, wadannan dalibai 58 za su tashi zuwa kasar Sin a watan Satumba, za su kuma kara ilminsu na digiri na farko ko biyu ko dakta a fannin injiniya, ilmin likitanci, ilmin noma, da ilmin gudanar da harkoki da dai saurasu.

Jakadan Sin dake kasar Zhou Pingjian, ya taya wa wadanda suka sami kyautar kudi karatun murna, tare da kara musu kwarin gwiwar ganewa idonsu yadda kasar Sin take yauzu, da himantu wajen karatunsu da cimma muradunsu, ta yadda za su ba da gudummawarsu ga ci gaban Nijeriya a nan gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China