Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta kaddamar da shirin yaki da cututtukan da ba a yada su
2019-08-08 10:12:10        cri
Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani shiri na shekaru 6 da nufin yin rigakafi da kuma dakile nau'in cututtukan da ba a yada su a duk fadin kasar, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwa daga jami'in gwamnatin kasar wacce aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba.

A cikin sanarwar da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya fitar, an bayyana cewa, cututtukan da ba a yada su sun kasance manyan kalubalolin kiwon lafiya dake damun kasar, kana suna yin mummunar illa ga ci gaban kasa da ma tattalin arzikin kasar.

An kaddamar da sabon shirin ne a ranar Talata, wanda ya kunshi wasu tsare-tsare daga sassa daban daban, ana fatan shirin zai taimaka wajen shawo kan barazanar cututtuka, kamar cutar ciwon zuciya, sankara, ciwon suga, da shakewar numfashi, da sauran cututtukan da ba a yada su wadanda ke damun al'ummar Najeriyar.

A cewar gwamnatin, shirin wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki wajen dakile cututtukan da ba a yada su, wanda zai taimakawa aniyar gwamnati, da kwararrun masana kiwon lafiya, da kuma marasa lafiya a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China